Assalamu Alaikum wa Rahmatullah. ’Yan uwa Musulmi, yau zan raba muku addu’a mai matukar tasiri wacce Annabi (SAW) ya ce tana dauke da Ismul A’azam—sunan Allah mafi girma.”
“Wannan addu’a tana da matukar tasiri domin tana ambaton Suratul Ikhlas, wacce ke bayyana tauhidi na Allah Madaukakin Sarki.”
(Karanta Addu’ar da Nutsuwa)
اللهم إني أسألك بأنك أنت الله لا إله إلا أنت الأحد الصمد الذي لم يلد ولم يولد ولم يكن له كفوا أحد
Fassara:
“Ya Allah, ina rokon Ka saboda Kai ne Allah, babu abin bautawa sai Kai, Kai ne ɗaya, Ubangijin da komai ke dogara da Shi, wanda bai haifa ba, ba a haife Shi ba, kuma babu wani da yake kama da Shi.”
”‘Yan uwa, wannan addu’a na daga cikin mafi karfi da Annabi (SAW) ya koyar. Ku yawaita karanta ta don samun albarka da kariya. Kada a manta a yi like, share, da follow domin karin ilimi!” ✍️Dr Shehu Muhammad